Romans 11

Ragowar Israʼila

1To, ina da tambaya: Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Israʼila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin. 2Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Eliya ba-yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Israʼila ya ce: 3“Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma nema su kashe ni”
1 Sar 19.10, 14
?
4Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Baʼal sujada ba.”
1 Sar 19.18
5Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri. 6In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.

7To, sai me? Abin da Israʼila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare, 8kamar yadda yake a rubuce cewa:

“Allah ya ba su ruhun ruɗewa,
idanu don su kāsa gani,
da kuma kunnuwa don su kāsa ji,
har yǎ zuwa yau.”
M Sh 29.4; Ish 29.10

9Dawuda kuma ya ce:

“Bari teburin cin abincinsu yǎ zama musu tarko,
sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.
10Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani,
bayansu kuma yǎ tanƙware har abada.”
Zab 69.22,23

Rassan Aure

11Har yanzu ina da tambaya: Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Alʼummai don a sa mutanen Israʼila su ji kishi. 12Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Alʼummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!

13Ina magana da ku ne fa Alʼummai. Tun da yake ni manzo ne ga Alʼummai, ina taƙama da aikin nan nawa, 14da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yǎ sa in ceci waɗansunsu. 15Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za ta zama in ba rai daga matattu ba? 16In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.

17In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan niʼimar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan, 18kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi laʼakari da wannan: Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. 19To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.” 20Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro. 21Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah: tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka. 23In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su. 24Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

Dukan Israʼila Za Su Tsira

25Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ʼyanʼuwa, domin kada ku ɗaga kai: Israʼila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Alʼummai masu yawa ya cika. 26Ta haka kuwa za a ceci dukan Israʼila, kamar yadda yake a rubuce cewa:

“Mai ceto zai zo daga Sihiyona;
zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.
27Wannan kuwa shi ne alkawarina da su
saʼad da na ɗauke musu zunabansu.”
Ish 59.20, 21; Ish 27.9; Irm 31.33,34

28Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu, 29gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa. 30Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu, 31haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku. 32Gama Allah ya ɗaure dukan mutane ga rashin biyayya don yǎ nuna jinƙai ga kowa.

Ɗaukakawa

33Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace!
Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike,
hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!
34“Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?
Ko kuwa yǎ ba shi shawara?”
Ish 40.13

35“Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu,
da Allah zai sāka masa?”
Ayu 41.11

36Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
Copyright information for HauSRK